Shugaban Hukumar Tsaron Cikin gida (DSS) na kasa, Oluwatosin Adeola Ajayi, ya kaddamar da Cibiyan koyar da Addinin Musulunci a kauyen Danbushiya na Garin Kaduna.
Makarantar Wanda Shugaban hukumar ta DSS na kasa ya Gina wacce aka sanya mata suna “Ahmed Bola Tinubu Darul Ilm Centre for Islamic Studies), an gina ta ne domin marayu da marasa galihu a cikin al’umma.
- Warware Basussuka: WAEC DA NECO Sun Saki Sakamakon Ɗaliban Zamfara Na Shekara Biyar
- Shekaru 10, Kofuna 16 Kevin De Bruyne Ya Yi Bankwana Da Manchester City
A jawabinsa, Shugaban na DSS ya bayyana cewa, ya Samar da cibiyarce domin bai wa al’ummar musulunci ilimi ingantacce da basu tarbiyya.
Shugaban Wanda Alhaji Ahmed Aliyu Zarma ya wakilta ya kara da cewa, wannan cibiya ba itace ta farko ba da shugaban ya fara ginawa ba, a cewarsa ya gina irinsu a sassa daban-daban a fadin kasar nan. Yana Mai Cewa, baya ga cibiyoyin koyar da addinin musulunci ya samar da makarantu a majami’un addnin kirista da gyaran makarantu da kuma tallafawa marayu da marasa galihu a cikin al’umma.
Zarma ya ce, sama da shekaru goma shugaban yana gudanar da irin wadannan Ayyukan tallafawa Rayuwar al’umma musamman marayu da marasa galihu a fadin kasar nan Baki daya.

A nasa jawabin, Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubukar lll Ya jinjiwa shugaban na DSS na ginawa da sadaukar da makarantar ga alummar musulmi duk da cewa, shi shugaban ba musulmi ba ne. Yace, “babu wata kasa a fadin Duniya da kirista da musulmi suke zama bisa fahimtar juna kamar Nijeriya”, inda yace hakan yana nuni da cewa abubuwa za su gyaru a kasar nan.
Sarkin Musulmi yace babu shakka lokaci ya kusa da za’a samu saukin rayuwa a fadin kasar nan duk da cewa al’umma suna fama da kuncin rayuwa.
A zantawarsa da manema labarai Jim kadan bayan kammala taron, shugaban kwamitin shirya taron, Shek Yusuf Sambo Rigachikun, ya yaba da kokarin shugaban DSS na sadaukar da makarantar ga al’ummar musulmi inda yace, matsayinsu na malaman addini zasu tabbatar da cewa an Samar da ilimi Mai nagarta da kula da tarbiyyar daliban dake karatu a makarantar.
Mahalarta taron sum hada da Mai Alfarma Sarkin Musulumi, Sultan Muhammadu Sa’ad Abubakar III; Ministan kasafin kudi, Abubakar Atiku Bagudu; Mataimakiyar Gwamnan Jihar kaduna, Hadiza Sabuwa Balarabe; Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli; Sarkin Birnin Gwari, Malam Zubairu Jibrin Mai Gwari, da dai sauran manyan Baki daga sassa daban-daban na kasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp