Da safiyar yau, wani mummunan rikici ya barke tsakanin jami’an ‘yansanda da wasu matasa a garin Rano, cikin ƙaramar hukumar Rano ta jihar Kano. Rikicin ya haifar da asarar rayuka, bayan da jama’a ke zargin cewa wani matashi ya mutu a hannun ‘yansanda.
Bayanin da ke fitowa daga garin ya nuna cewa wasu fusatattun matasa sun je ƙone ofishin ‘yansanda a Rano, bisa zargin cewa ‘yansandan sun kashe wani saurayi mai suna Hassan Salisu, bayan da aka kama Salisu bisa zargin karya ka’idojin hanya da kuma yin ganganci da mashin mai kafa biyu.
- Fitaccen Fastan Kaduna Rabaran Azzaman Ya Mutu A Haɗarin Mota
- Akwai Alamar Tambaya A Sake Lalacewar Matatar Mai Ta Fatakwal A Karo Na 2, Bayan Kashe Dala Biliyan 1.5
Daga cikin matasan da suka kona ofishin, wasu sun sami raunuka yayin da ‘yansada sukai harbin kan mai-uwa-da-wabi kuma tuni aka garzaya da su asibiti.
Kakakin Yansandan jihar Kano, DSP Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce rundunar za ta gudanar da bincike mai zurfi don gano musabbabin rikicin da kuma aiwatar da adalci. Ya kuma yi kira ga jama’a da su nuna haƙuri yayin da hukumar ke gudanar da binciken.
Wasu masu fada aji sun yi kira da a gudanar da bincike mai inganci don hana irin wannan rikicin a nan gaba. Haka kuma, akwai bukatar gwamnati da hukumomi su saurari korafin jama’a game da halin da ‘yansanda ke ciki, domin tabbatar da zaman lafiya da adalci a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp