Hukumar babban birnin tarayya Abuja (FCTA) ta aiwatar da gargadin da ta yi a ranar Litinin ta hanyar rufe hedikwatar jam’iyyar PDP ta Wadata Plaza da ke Abuja.
Matakin ya biyo bayan zargin gazawar da jam’iyyar ta yi kan biyan kudaden harajin kasa na sama da shekaru 25.
- Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Wanda Ya Kona Masallata A Kano
- Kakakin Majalisa Ya Janye Ƙudurin Dokar Tilastawa Ƴan Nijeriya Yin Zaɓe
A baya dai mahukuntan babban birnin tarayya Abuja sun sanar da jam’iyyar PDP domin ta warware basussukan da aka dade ana bin su.
Matakin na FCTA ya kara jaddada daukar tsauraran matakai kan wadanda suka saba ka’idojin amfani da filaye a babban birnin kasar.
Jami’an sun ce, rufewar za ta ci gaba da aiki har sai an warware basussukan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp