Wani bincike da kafar yada labaru ta CGTN ta gudanar a tsakanin mutane 1,000 daga manyan kasashe 10 na tsibiran tekun Fasifik, a yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen Sin da tekun Fasifik karo na uku ya nuna cewa, wadanda suka bayyana ra’ayoyin sun yi nazari mai kyau game da ci gaban falsafar zamanantar da kasar Sin da kuma nasarorin da ta samu.
A cikin shekaru da dama da suka gabata, kasar Sin ta ci gaba da zurfafa huldar tattalin arziki da cinikayya da kasashen tsibiran Fasifik. Daga shekarar 1992 zuwa 2021, hada-hadar cinikayya tsakanin Sin da abokan huldar diflomasiyyarta a tsibiran Fasifik sun karu daga dala miliyan 153 zuwa dala biliyan 5.3, inda aka samu kari fiye da sau 30.
- Shugaban Kasar Kenya: FOCAC Ya Samar Da Damammaki Ga Sin Da Afirka Wajen Inganta Hadin Kansu Da Samun Moriya Tare
- Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Wanda Ya Kona Masallata A Kano
Bisa kididdigar da aka yi, kashi 93.6 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyi daga kasashen tsibiran tekun Fasifik, suna kallon babbar kasuwar kasar Sin a matsayin wata dama ga kasashensu, yayin da kashi 92.2 cikin dari kuma suka yi amannar cewa kasashensu sun ci gajiyar mu’amalar tattalin arziki da ta cinikayya tare da kasar Sin.
Bayan haka, masu bayyana ra’ayoyin na tsibiran Fasifik sun yi matukar yabawa da karfin fasahar kere-keren kasar Sin, inda kashi 91.4 cikin dari suka yaba da kwarewar kasar a fannin kimiyya da fasaha. Musamman bangaren motocin sabbin makamashi na kasar Sin, da baturan ma’adanan Lithium, da kayayyakin fasahar kirkirarriyar basira ta AI kamar manhajar DeepSeek, da na makamashin hasken rana duka sun burge su kwarai da gaske.
Kafar yada labaru ta CGTN tare da hadin gwiwar jami’ar Renmin ta kasar Sin ne suka gudanar da binciken, ta hannun Tsangayar Nazarin Sadarwa a Sabon Zamani ta Kasa da Kasa. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp