Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da shirye-shirye, domin harba na’urar binciken samaniya ta kasar Sin mai lakabin Tianwen-2, a ranar Alhamis 29 ga watan nan, na’urar da ake fatan za ta samar da bayanai game da sirrin dake tattare da tauraron dake kusa da sararin samaniyar bil adama, da karamin tauraron dake kewaya da’irar dake shiyyar, kamar dai yadda hukumar kula da binciken sararin samaniya ta kasar Sin ko CNSA ta sanar a Litinin din nan.
Ana sa ran na’urar Tianwen-2, za ta tattaro samfura daga tauraro mai lamba 2016HO3, aikin da zai zamo irinsa na farko a fannin, kana zai kewaya karamin tauraron “comet 311P”.
Yanzu haka dai ana ci gaba da shirye-shirye domin tabbatar da nasarar harba na’urar Tianwen-2, daga cibiyar harba kumbuna ta Xichang a lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp