Shugaban kasa, Bola Tinubu ya rubutawa majalisar wakilai wasika, inda ya nemi amincewarta kan bukatar amso wani sabon bashi daga waje, da ya kai dala biliyan 21.5 da kuma lamuni na cikin gida na Naira biliyan 757.9
Tinubu, a cikin wata wasika da kakakin majalisar, Abbas Tajudeenya ya karanta a zaman majalisar a ranar Talata, ya ce, za a yi amfani da kudin ne wajen inganta dukkanin bangarorin more rayuwa masu muhimmanci musamman, noma, kiwon lafiya, ilimi, samar da ruwan sha, tsaro, samar da ayyukan yi, da gyare-gyare da sauransu.
- Rundunar Ƴansanda Ta Gayyaci Jami’anta Da Bidiyonsu Ya Yaɗu Suna Karɓar Cin Hancin Naira 5000
- Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ɗaga Likafar Kwalejin Fasaha Ta Kabo Zuwa Jami’a
Shugaban kasan, ya ce jimillar kudaden da ake shirin amsowa daga Lamunin wajen sun hada da dala miliyan 21,543,647,912, da Yuro biliyan 2,193,856,324.54, da Yen biliyan 15, baya ga tallafin Yuro miliyan 65.
Tinubu ya bayyana cewa, rancen da ake shirin amsowa na da matukar muhimmanci, domin dakile mummuman tasirin da cire tallafin man fetur ya yi akan tattalin arzikin kasar.
Tinubu ya kara da cewa, za a yi amfani da wadannan kudade ne zuwa muhimman ayyukan samar da ababen more rayuwa, da shirye-shiryen ci gaban kasa baki daya a fadin jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp