An yi garkuwa da Basaraken Sangarin Dari, Basaraken Al’ummar Dari da ke karamar Hukumar Kokona a Jihar Nasarawa, Emmanuel Omanji.
An ce wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a tantance ko su waye ba ne suka sace Sangarin Darin a gidansa da safiyar ranar Laraba.
- AU Ta Jinjinawa Goyon Bayan Sin Ga Ci Gaban Nahiyar Afrika
- Tinubu Ya Yi Ƙoƙari, Gyaran Nijeriya Aikin Kowa Da Kowa Ne – Buhari
Shaidun gani da ido, sun ce ‘yan bindigar sun afka garin, inda suka yi ta harbe-harbe a sama sannan suka nufi gidan Sangarin, daga nan suka tafi da shi.
Wakilinmu ya tattaro cewa, babu wanda ya rasa ransa yayin harin amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a san inda basaraken ya ke ba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda, SP Ranham Nansel ya tabbatar da sace Basaraken.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp