ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gyaran Jiki Da Kyawun Fata (2)

by Bilkisu Tijjani
6 months ago
Jiki

Illar Rashin Gyaran Jiki:

Yana da matukar muni ga kowanne dan’Adam ya zama mai rashin kulawa da gyaran jiki musamman ma ga ma’aurata domin illar rashin gyaran jikin ya fi ga ma’aurata da kuma ‘ya mace.

A zahiri ‘ya mace ta kan fuskanci matsala a gidan aurenta kullum cikin rigima da tashin hankali a tsakaninta da maigidanta, iyaye suna ta faman zarya wajen sulhunta tsakaninsu amma abu ya gagara, a karshe sai dai ka ji aure ya rabu.

ADVERTISEMENT

Anan Fa aiki ne na iyaye mata:

A matsayinki na uwa ko ‘ya ko ‘yar uwa ko kawa yana da kyau idan kika ga cewa ga ‘yarki ko ‘yar uwarki ko kanwarrki ko kawarki ana ta faman zarya na sulhunta aurenta a tsakaninta da mijinta abu ya ki jituwa, to ki yi kokarin gano shin mene ne matsalarta.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za Ku Gyara Kanku

Maganin Nankarwa (4)

Ta hanyar da za ki gano kuwa ita ce, ki kai mata ziyara ta wuni daya kuma idan kin je ki kula da yaya yanayin huldodinta da kuma gyaran jikinta suke a cikin gidanta, ta nan ne za ki fahimci matsalar rashin jituwarta da mijin na ta.

Domin ita matsalar rashin kulawa da gyaran jiki wani namiji ba zai iya bude baki ya fada ba.

Koda ita matar ma ba zai iya fada mata ba sai dai kurum ka ga ana rigima ita tana ta ganin yana yi mata wulakanci shi kuma ga abin da yake gani daban, don haka yana da matukar muhimmancin ga ma’aurata da su himmantu wajen gyara jiki ba su kadai ba, har da wanda ba su yi aure ba domin addinin musulunci ma ya zo mana da nuni na kulawa da tsafta.

Sirrin Mace

Kowacce mace ta san cewa sirri ne a tare da ita sutura al’aurarta musamman ma ga mace mai aure

Yana daga cikin sutura al’aurarta da kula da gyaranta domin ita ce babbar hanya da idan ba kya kulawa da gyara ta hakika za ki fuskanci illolo daban-daban kamar za ki ji haka kawai kina wari.

Maigida zai rika gudunki, za ki ga kina fitar da ruwa mai kazanta a yayin al’ada kuma doyi ma za ki rika yi don ko dakinki aka shiga za a ji yana ta doyi.

To amma idan kina kula da tsafta hakika duka wannan za ki ji kin rabu da shi, kuma maigida ba zai rika baya-baya da ke ba, bare har ta kai ga rabuwar aure.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Za Ku Gyara Kanku
Ado Da Kwalliya

Yadda Za Ku Gyara Kanku

November 15, 2025
Maganin Nankarwa (4)
Ado Da Kwalliya

Maganin Nankarwa (4)

November 8, 2025
Yadda Za A Magance Amosanin Baki
Ado Da Kwalliya

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

October 4, 2025
Next Post
CMG Ya Watsa Shirin Musamman Na Bikin Duanwu Na 2025

CMG Ya Watsa Shirin Musamman Na Bikin Duanwu Na 2025

LABARAI MASU NASABA

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

November 16, 2025
Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

November 16, 2025
Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

November 16, 2025
Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

November 16, 2025
Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

November 16, 2025
DSS

Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato

November 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.