Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet), ta ce ana iya samun ambaliya a wasu jihohin ƙasar nan, musamman a Arewacin Nijeriya da yankin Arewa ta Tsakiya, a cikin watan Yunin shekarar 2025.
NiMet ta bayyana hakan ne cikin wani rahoton hasashen yanayi da ta fitar a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni, 2025.
- An Yi Balaguro Miliyan 657 A Tsakanin Yankunan Kasar Sin Lokacin Bikin Duanwu Na Bana
- Ministan Tsaron Singapore: Sinawa Ne Za Su Iya Tantance Batun Taiwan
Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da juyayin ambaliya da ta faru a Jihar Neja, wadda ake zargin ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 500.
NiMet ta bayyana cewa za a iya samun ruwan sama mai yawa a jihohin Nasarawa, Filato, Bauchi, Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi da kuma Abuja.
Wannan yanayi zai iya haddasa ambaliya a yankunan da ke cikin hatsari.
Hukumar ta buƙaci jama’a da su kasance cikin shiri tare da bibiyar sabbin rahotannin yanayi da ta ke fitarwa.
Ta kuma ja hankalin hukumomin da ke kula da madatsun ruwa da su saka ido kan matakin ruwa domin gujewa cike-ciken da ka iya haddasa ambaliya.
Rahoton ya ƙara da cewa jihohin kudancin Nijeriya da kuma na Arewa ta Tsakiya za su riƙa samun ruwan sama da iska a kai a kai.
Sai dai NiMet ta ce jihohin Kwara, Kogi, Neja, Nasarawa, Benuwe, Taraba, Adamawa, Kaduna, Kano, Katsina, Sakkwato, Edo, Delta da Abuja ba za su samu ruwan sama da yawa kamar yadda aka saba ba.
Hukumar ta buƙaci manoma da su yi amfani da dabarun zamani da ilimin kimiyya wajen gudanar da harkokin noma a wannan daminar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp