Wasu shedu da jami’an ‘yan sanda sun bayyana cewa, an harbe wani malamin addinin Islama, Sheikh Goni Aisami Gashua, a hanyarsa daga jihar Kano zuwa garin Gashua a jihar Yobe.
Ana zargin wasu jami’an soji biyu ne suka kashe malamin a ranar Asabar.
- An Shiga Alhinin Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Sheikh Goni Aisami Gashuwa, A Yobe
- Kwamishinan Yobe, Goni Bukar, Ya Rasu A Hadarin Mota
Wata majiya ta shaida wa LEADERSHIP ta wayar tarho cewa an harbe, Sheikh Goni Aisami Gashua, a cikin motarsa.
A cewar majiyar, lamarin ya faru ne a Jaji-Maji, mai tazarar kilomita kadan daga garin Gashua da misalin karfe 10 na safiyar ranar Asabar.
Daya daga cikin makusantansa, Hon. M.K. Gogaram ya shaidawa LEADERSHIP cewa jami’an Soja biyu da ake zargin sun yi harbin kan mai uwa da wabi, daga bisani su dauke gawarsa daga motarsa ​​suka yi watsi da ita a bakin titi.
Tuni dai aka yi jana’izar marigayi Malamin addinin Musulunci, Sheikh Aisami, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
A halin da ake ciki, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da kama mutanen biyu.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne da laifin kashe malamin.