Fadar shugaban kasa ta fara amincewa da matakan biyan bashin naira tiriliyan 2 na kudaden da kamfanonin samar da wutar lantarki ke binta kafin zuwan zango na gaba, a wani yunkuri da gwamnatin ke yi daidaita da samar da wuta yadda ya dace a Nijeriya.
Wakiliyar mai bai wa shugaban kasa shawara kan makamashi, Eriye Onagoruwa, ita ce ta shaida hakan a ranar Litinin yayin taron masu ruwa da tsaki a harkar samar da wuta a Nijeriya karo na biyu na 2025, wanda hukumar kula da bin dokokin wutar lantarki NERC ke amsar bakwanci.
- Ribadu Ya Kara Jaddada Gargadinsa Kan Biyan Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane
- Namibia Za Ta Karfafa Hulda Da Sin Yayin Baje Kolin Cinikayya Da Tattalin Arziki
Onagoruwa ta ce fadar shugaban kasa ta lura da bukatar gaggawa da ake da shi na neman biyan basukan domin dorewar kamfanonin samar da wutar lantarki (GenCos) da kuma kyautata harkokin samar da wuta. Ta bayyana cewar ana bibiyar wasu basuka saboda kokarin gwamanti na shawo kan matsalolin kasafin kudi.
Duk da cewa ba ta bayyana ranar da za a biya kudin ba, Onagoruwa ta nuna kwarin gwiwarta na cewa za a biya kudaden kafin zango na gaba, ta kuma ce za a samar da matakin da ake ciki nan da watanni uku masu zuwa.
“Ina fatan kafin zaman NESI na gaba, zan samu damar shelanta jerin yadda biyan kudin zai kasance,” ta shaida.
Idan za a tuna dai kamfanonin samar da wutar lantarki a kwanakin baya sun gargadi gwamnatin tarayya kan ci gaba da rike musu basuka wanda yanzu ke neman kai wa naira tiriliyan 4.
A kwanakin baya ne kwamitin majalisar datawa mai kula da wutar lantarki ya nuna damuwarsa kan matsalar karancin wutar lantarki da ta dabaibaye bangaren wutar lantarki, inda ya koka da yadda karancin kudin wutar lantarki a masana’antar, ya nuna cewa gwamnati na rike da kudaden kamfanonin da ke samar da wutar lantarki kusan naira biliyan 200 a duk wata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp