• English
  • Business News
Tuesday, July 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Halarci Babban Taron MDD Kan Tekuna

by CGTN Hausa and Sulaiman
2 months ago
in Daga Birnin Sin
0
Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Halarci Babban Taron MDD Kan Tekuna
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya halarci babban taron MDD kan tekuna karo na 3, wanda aka gudanar a kasar Faransa, tsakanin ranakun 8 zuwa 9 ga watan nan da muke ciki, bisa gayyatar da aka yi masa.

A jawabin da ya gabatar yayin taron muhawara da aka yi, Han Zheng ya ce, a bana, aka cika shekaru 80 da kafuwar MDD, don haka zai fi kyau a yi amfani da wannan dama ta gudanar da babban taron MDD kan tekuna, wajen daidaita aikin kare da raya dauwamammen ci gaban albarkatun tekuna, ta yadda za a gina makomar bil Adama ta bai daya.

  • Sojoji Sun Kashe Babban Kwamandan Boko Haram A Jihar Yobe
  • Ba Mu Iya “Gina” Ayaba A Amurka

Ya kara da cewa, da farko, ya kamata a kafa yanayin zaman lafiya da tsaron tekuna cikin hadin gwiwa. Sa’an nan kuma, a inganta aikin amfani da albarkatun tekuna domin tallafawa juna. Haka kuma, ya kamata a karfafa wayewar kai da mu’amala kan harkoki masu nasaba da tekuna. A karshe kuma, ya kamata a dukufa wajen kiyaye tsabtar tekuna.

Bugu da kari, ya ce, kasar Sin za ta karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa, ta hanyar amfani da Asusun raya kasashen duniya da hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, domin gudanar da ayyukan da suka shafi tekuna, yayin raya harkokin da abin ya shafa ta hanyoyin kare muhalli. Haka kuma, kasar Sin tana fatan ganin aiwatarwar da yarjejeniyar kiyaye nau’o’in halittun tekuna cikin sauri, kuma bisa dukkan fannoni.

A yayin taron, Han Zheng ya kuma gana da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, da babban magatakardan MDD Antonio Guterres. (Mai Fassara: Maryam Yang)

Labarai Masu Nasaba

Sojojin Sin Sun Bi Sahun Shiga Ayyukan Ba Da Agajin Ambaliyar Ruwa

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Taron Wanzar Da Zaman Lafiya Na Matasan Kasa Da Kasa

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Mutum 10 Sun Mutu Sakamakon Harbe-harbe A Makarantar Sakandire A Kasar Austriya

Next Post

Gwamna Zulum Ya Bayar Da Tallafin Miliyan 300 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Mokwa

Related

Sojojin Sin Sun Bi Sahun Shiga Ayyukan Ba Da Agajin Ambaliyar Ruwa
Daga Birnin Sin

Sojojin Sin Sun Bi Sahun Shiga Ayyukan Ba Da Agajin Ambaliyar Ruwa

11 minutes ago
Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Taron Wanzar Da Zaman Lafiya Na Matasan Kasa Da Kasa
Daga Birnin Sin

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Taron Wanzar Da Zaman Lafiya Na Matasan Kasa Da Kasa

1 hour ago
An Fitar Da Kudaden Farfado Da Sassan Birnin Beijing Da Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Shafa
Daga Birnin Sin

An Fitar Da Kudaden Farfado Da Sassan Birnin Beijing Da Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Shafa

2 hours ago
Xi Ya Yi Kira Da A Yi Azamar Kare Rayukan Al’umma Yayin Da Ake Fuskantar Ibtila’in Ambaliya A Wasu Sassan Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Xi Ya Yi Kira Da A Yi Azamar Kare Rayukan Al’umma Yayin Da Ake Fuskantar Ibtila’in Ambaliya A Wasu Sassan Kasar Sin

3 hours ago
An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025

22 hours ago
Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa
Daga Birnin Sin

Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa

23 hours ago
Next Post
Gwamna Zulum Ya Bayar Da Tallafin Miliyan 300 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Mokwa

Gwamna Zulum Ya Bayar Da Tallafin Miliyan 300 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Mokwa

LABARAI MASU NASABA

Sojojin Sin Sun Bi Sahun Shiga Ayyukan Ba Da Agajin Ambaliyar Ruwa

Sojojin Sin Sun Bi Sahun Shiga Ayyukan Ba Da Agajin Ambaliyar Ruwa

July 29, 2025
Babu Wata Karamar Hukumar Dake Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang

Babu Wata Karamar Hukumar Dake Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang

July 29, 2025
Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Taron Wanzar Da Zaman Lafiya Na Matasan Kasa Da Kasa

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Taron Wanzar Da Zaman Lafiya Na Matasan Kasa Da Kasa

July 29, 2025
Morocco Ta Shigar Da Ƙara Kan Nasarar Super Falcons A Gasar WAFCON

Morocco Ta Shigar Da Ƙara Kan Nasarar Super Falcons A Gasar WAFCON

July 29, 2025
An Fitar Da Kudaden Farfado Da Sassan Birnin Beijing Da Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Shafa

An Fitar Da Kudaden Farfado Da Sassan Birnin Beijing Da Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Shafa

July 29, 2025
Matashi Ya Kashe Surukarsa Saboda Shigarta Cikin Sha’anin Aurensu

Matashi Ya Kashe Surukarsa Saboda Shigarta Cikin Sha’anin Aurensu

July 29, 2025
Xi Ya Yi Kira Da A Yi Azamar Kare Rayukan Al’umma Yayin Da Ake Fuskantar Ibtila’in Ambaliya A Wasu Sassan Kasar Sin

Xi Ya Yi Kira Da A Yi Azamar Kare Rayukan Al’umma Yayin Da Ake Fuskantar Ibtila’in Ambaliya A Wasu Sassan Kasar Sin

July 29, 2025
Birtaniya Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Mutane 33 A Zamfara

Birtaniya Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Mutane 33 A Zamfara

July 29, 2025
Mai Cin Moriyar Kai Da Mai Cin Moriyar Juna

Mai Cin Moriyar Kai Da Mai Cin Moriyar Juna

July 29, 2025
Kar Ka Zuga Ƴan Arewa Kan Tinubu — Nabena Ya Gargaɗi Kwankwaso

Kar Ka Zuga Ƴan Arewa Kan Tinubu — Nabena Ya Gargaɗi Kwankwaso

July 29, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.