Gwamnatin jihar Kogi ta jaddada kudirinta na yaki da rashin tsaro tare da yin kira ga jama’a da masu yada labarai da kuma ‘yan siyasa da su guji yada firgici domin cimma muradun siyasa a kalubalen tsaron jihar.
Gargadin ya biyo bayan yawaitar sace-sacen mutane da kashe-kashe a baya-bayan nan, musamman a yankin Yammacin jihar.
- Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Halarci Babban Taron MDD Kan Tekuna
- Sarki Sanusi II Ya Yi Hawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda Na Haramta Hawan Sallah A Kano
Kwamishinan yada labarai da sadarwa, Kingsley Fanwo, a Lokoja a ranar Talata, ya ce, gwamnatin ta samu nasarori a yaki da ta’addanci kawo yanzu a jihar.
LEADERSHIP ta tuna cewa, gwamnatin jihar da jami’an tsaro sun fuskanci matsin lamba daga mazauna yankunan da lamarin ya shafa domin shawo kan lamarin.
Fanwo, ya ba da tabbacin cewa, gwamnati ta yi shiru, amma tana samun nasara a yakin da take da masu aikata laifuka ta karkashin kasa, musamman masu garkuwa da mutane a jihar.
Ya ce, nasarar da gwamnati ta samu ya biyo bayan ingantattun tsare-tsare da zurfafa hadin gwiwar hukumomin tsaro da nufin tabbatar da tsaro da walwalar kowane dan jihar Kogi.
Yayin da take jajantawa iyalan wadanda hare-haren na baya-bayan nan ya shafa, gwamnatin jihar ta jaddada cewa, bai kamata a yi amfani da irin wadannan kalubalen wajen yada labaran karya ko firgita jama’a ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp