Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta ragu zuwa kashi 22.97 a watan Mayu 2025, daga 23.71 a watan Afrilu.
Wannan na nuna cewa farashin kayayyaki na ci gaba da tashi, amma ba a hankali ba kamar yadda yake a baya ba.
- Sin Ta Yi Kira Ga Iran Da Isra’ila Su Dauki Matakan Dakile Ruruwar Wutar Rikicinsu Nan Da Nan
- FCCPC Ta Sammaci Air Peace Kan Rashin Maido Da Kuɗin Tikitin Jirgin Da Aka Soke Tafiyarsa
Farashin abinci ya tashi da 2.19 a watan Mayu idan aka kwatanta da watan Afrilu, amma hauhawar farashin kayan abinci na shekara-shekara ya sauka zuwa kashi 21.14 daga 40.66 a watan Mayun 2024.
NBS ta ce wannan ragi ya faru ne sakamakon canji a tsarin lissafin hauhawar farashi.
A birane, hauhawar farashi ya kasance 23.14, yayin da a karkara ya tsaya a kashi 22.70 duka suna ƙasa da na shekarar da ta gabata.
Wannan ya nuna ragin hauhawar farashi a faɗin ƙasar nan.
Masana na ganin wannan ragi a matsayin alamar ci gaba ga tattalin arziƙi, sai dai har yanzu ‘yan Nijeriya da dama na fama da tsadar rayuwa, musamman wajen samun kayan abinci da wasu muhimman abubuwan buƙara na yau da kullum.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp