A wani gangamin magance aikata laifukan zamba da damfara ta shafukan intanet da kasar Sin ta kaddamar a fadin kasar baki daya, ‘yan sandan kasar ta Sin sun fatattaki laifuka 294,000 a shekarar 2024, inda suka kama mutane da dama da ake zargi ciki har da shugabanni gungu-gungu fiye da 570, da masu samar musu da kudi, da kuma kasurguman da ke da hannu a wannan ta’asar.
‘Yan sanda sun durfafi cibiyoyin sadarwa na masu aikata laifuka da ke ba da haramtaccen tallafi ga aikata ayyukan zamba a kasashen ketare. A cewar ma’aikatar kula da tsaron al’umma, wadannan kungiyoyin sun tafka ta’asa masu yawa da suka hada da tallata laifukan a shafin intanet, da satar kudi, da amfani da fasaha, da kuma taimakawa wajen saukake hanyoyin tsallaka kan iyakokin kasa.
Tun daga farkon shekarar 2024, cibiyar yaki da zamba ta kasar Sin ta kara kaimi wajen yin gargadi a kan lokaci da kuma daukar matakan dakile ta’asar ta hanyar amfani da fasahohin zamani, inda ta ba da sanarwa game da hakan sau miliyan 1.8. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp