A daren ranar Talata ne aka sake kai hari gidan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da aka dakatar, mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya a gidansu dake Ihima a karamar hukumar Okehi a jihar Kogi.
A wata sanarwa da ofishin yada labarai na Natasha Akpoti-Uduaghan ya fitar ranar Laraba a Abuja, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun lalata tagogi da dama. Sai dai kuma da gaggawar jami’an ‘yansandan yankin, da ‘yan banga, da kuma matasan yankin, an samu nasarar fatattakar maharan tare da kama wani acikinsu.
- Dan Wasan Gaban Chelsea, Murdyk Ka Iya Shafe Shekaru 4 Ba Tare Da Ya Buga Wasa Ba
- “Ruhin Sin Da Tsakiyar Asiya” Ya Jagoranci Bude Wani Sabon Babi Na Hadin Gwiwar Yanki
Wanda aka cafken, mai suna Suberu Jose wanda ake kyautata zaton yana da alaka da abokin hamayyar siyasar ‘yar majalisar kuma sananne ne acikin al’ummar yankin. Rahotanni sun ce ya amsa laifinsa kuma ya amince cewa, wannan shi ne karo na uku da ya kasance acikin maharan da suka kai hari gidan dangin ‘yar majalisar.
Idan dai za a iya tunawa, a baya an kai hari gidan dangin Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 15 ga Afrilu, 2025, ba tare da an kama ko daya daga cikin maharan ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp