Shugaban hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS), Zacch Adedeji, ya ba da umarnin tsawaita ayyukan ofishin haraji zuwa karshen makon wannan watan na Yuni.
Tare da umarnin, ana sa ran ofisoshin na haraji za a fara bude su tun daga karfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma, ranar Asabar kuma daga 12:00 na rana zuwa 4:00 na yamma, haka nan ma; ranar Lahadi har zuwa karshen watan na Yuni.
- EFCC Ta Kama Tsohon Kakakin Majalisar Filato Da Wasu ‘Yan Majalisa 14 Bisa Zargin Almundahana
- EFCC Ta Miƙa Gidaje 750 Na Emefiele Da Ta Ƙwace Ga Ministan Gidaje
Umarnin, a cewar wata sanarwa da mashawarci na musamman ga shugaban hukumar harajin ya fitar, Dare Adekanmbi, wani bangare ne na kudirin Adedeji na daidaita manufofin hukumar tare da daukar matakai na zahiri.
Sanarwar ta bayyana cewa, gudanar da aikin a ranakun karshen mako da zai fara daga ranar 14 ga Yuni, ya kuma kare a ranar 29 ga watan Yunin, “sannan manufar ita ce, don taimaka wa kamfanonin da ba su samu damar shigar da bayanan harajin a karshen wata ba, kafin cikar wa’adin da aka diba musu.
“Kamar yadda kuka sani, watan Yuni ne karshen kololuwar lokacin cikar harajin kamfanoni na shekara, inda ake sa ran masu biyan haraji da dawa, wadanda shekarar kudadensu ta kare a ranar 31 ga watan Desamba, za su gabatar da bayanan harajin nan da 30 ga watan Yuni.
“Domin saukaka wannan tsari ga masu biyan haraji da kuma kara yawan karbar harajin a cikin irin wannan mawuyacin lokaci, hukumar ta amince da tsawaita ayyukan ofisoshin harajin zuwa karshen mako na watan Yunin 2025,” in ji umarnin da shugabannin uku suka sanya wa hannu, in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp