Hukumar kula da ingancin fasahohin samar da lantarki ta duniya (IEC) ta ce kasar Sin za ta jagoranci samar da kundin tsarin amfani da sabbin makamashin samar da lantarki na kasa da kasa na farko.Â
Hukumar ta bayyana haka ne yayin taron daidaita fasahohin samar da lantarki na duniya da ya gudana a birnin Nanjing na lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin.
Ba kamar tsarin makamashi da aka saba da shi na kwal ba, wannan kundi zai mayar da hankali ne kan abubuwa masu samar da makamashi mai tsafta kamar iska da haske da nukiliya da tsirrai.
A cewar hukumar IEC, an shafe shekaru da dama kasar Sin na daukar matsayi na daya a duniya a bangaren karfin tashoshin lantarki da samar da lantarki daga sabbin makamashi. (Mai fassarawa: Fa’iza daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp