Dakarun sojin Nijeriya sun samu gagarumar nasara a yaƙin da suke yi da ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas.
A cikin makonni uku da suka wuce, rundunar “Operation Hadin Kai” ta kashe ‘yan ta’adda 600, ciki har da manyan kwamandojin Boko Haram da ISWAP.
- Majalisar Dattawa Na Nazarin Shawarwari 31, Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi
- EFCC Ta Kama Tsohon Babban Jami’in NNPC Kan Zargin Satar Dala Biliyan 7.2
Wannan nasarar ta biyo bayan ci gaba da yaƙi da ta’addanci da sojojin suka yi tun farkon watan Yuni, bayan da ‘yan ta’adda suka kai hare-hare har sau 12 a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji da fararen hula da dama.
A makon farko na watan Yuni, sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 94.
Amma kuma, jami’an tsaro 20 ciki har da sojoji da ‘yan sa-kai sun rasu, yayin da wasu sama da 20 suka jikkata.
Ko da yake sojojin na samun nasara, har yanzu mutane a yankin suna cikin fargaba saboda halin da ake ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp