Babban Hafsan Sojojin Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya bayyana cewa hedkwatar tsaro (DHQ) za ta tura dakaru na musamman sama da 800 da aka horar da su zuwa wuraren da ake fama da kalubalen tsaro a fadin kasar nan.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a taron horas da sojoji a Abuja ranar Laraba.
- An Kashe ‘Yan Ta’adda 6,260, An Ceto Mutane 5,365 Acikin Shekaru Biyu – Hedikwatar Tsaro
- Gwamnan Sakkwato Ya Kaddamar Da Aikin Gina Gidaje 500 Don Rage Matsalar Rashin Gida
Ya bayyana cewa dakarun na musamman sun samu horo na musamman domin tunkarar barazanar da ke kunno kai a yanzu.
Wasu jihohin da suka hada da Benuwe, Filato, da Borno, a ‘yan kwanakin nan sun samu tabarbarewar tsaro, lamarin da ya sa sojoji da sauran jami’an tsaro suka kara zage damtse wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da kalubalen tsaron ke kara ta’azzara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp