Mutane 4 ne suka mutu yayin da wasu 10 suka samu raunuka bayan da wata mota kirar Isuzu dauke da fasinjoji daga Damboa zuwa Maiduguri a jihar Borno ta taka wani Bam da ake kyautata zaton ‘yan ta’addar Boko Haram ne suka dasa shi akan hanyar.
Lamarin ya faru ne a kauyen Komala da ke Konduga a karamar hukumar Konduga a jihar Borno.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Kasuwa da Ɗan Banga A Kwara
- Manchester United Da Everton Na Zawarcin Wilfred Ndidi
LEADERSHIP ta rahoto cewa, a wani lamari makamancin haka a ranar Juma’ar da ta gabata a daidai Konduga, wani dan kunar bakin wake da ake kyautata zaton dan kungiyar Boko Haram ne ya tayar da bam a wata kasuwar kifi mai cunkoson jama’a inda ya kashe mutane 12 tare da jikkata wasu 18.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Borno (PPRO), Nahum Kenneth Daso ya raba wa manema labarai a ranar Laraba a Maiduguri, ta ce an kwashe gawarwakin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata zuwa asibitin kwararru na jihar da ke Maiduguri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp