ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Kasuwa da Ɗan Banga A Kwara

by Sadiq
1 year ago
Kwara

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe wani ɗan kasuwa mai shekaru 45, Alhaji Dauda Ismail, a garin Okuta da ke ƙaramar hukumar Baruten, a Jihar Kwara.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun sace Alhaji Dauda wanda ke kasuwancin kayan gona, kuma suka kashe shi a ranar Litinin a unguwar Takare da ke Okuta.

  • Sayar Da Makamai: Goyon Baya Ko Cin Riba?
  • Shugabannin PDP Sun Ziyarci INEC Kan Neman Sanin Ka’idojinta

Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar da yammacin ranar Talata.

ADVERTISEMENT

Ta ce ‘yansanda sun kashe ɗaya daga cikin masu garkuwar a musayar wuta.

Ta ƙara da cewa wani ɗan banga mai suna Haruna Tasusuno shi ma an harbe shi a yayin fafatawar, kuma an garzaya da shi asibitin garin Okuta, inda aka tabbatar da mutuwarsa.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

A cewar sanarwar, a ranar 22 ga watan Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 10:40 na dare, wasu mutane huɗu ɗauke da bindigu sun kai farmaki gidan Alhaji Dauda, inda suka yi harbe-harbe sannan suka sace shi suka tafi da shi zuwa wani waje da ba a sani ba.

Nan da nan jami’an ‘yansanda, sojoji, ‘yan banga da masu farauta suka haɗa tawaga domin shiga daji don ceto mutumin.

Washegari da safe, ranar 23 ga watan Yuni, da misalin ƙarfe 7 na safe, tawagar ta haɗu da masu garkuwar a ƙauyen Korori.

Sai da aka yi musayar wuta, inda aka kashe ɗaya daga cikinsu, aka ƙwato bindiga ƙirar AK-47 mai harsashi 13.

Sauran kuwa suka tsere cikin daji, kuma ana ci gaba da nemansu.

Abin takaici, ɗan banga Haruna Tasusuno ya samu rauni sakamakon harbi, inda aka garzaya da shi asibiti kuma aka tabbatar da rasuwarsa daga baya.

An samu Alhaji Dauda kwance a daji cikin jini da raunukan sara da adda a jikinsa, kuma likita ya tabbatar da cewa ya rasu.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
KAROTA Ta Kama Matasa 5 Kan Ɗaukar Bidiyo A Kan Hanya A Kano

KAROTA Ta Kama Matasa 5 Kan Ɗaukar Bidiyo A Kan Hanya A Kano

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.