Gwamnatin jihar Kano ta ayyana ranar Alhamis 26 ga watan Yunin 2025 a matsayin ranar hutu domin murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1447.
Hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya.
- Gwamnan Jigawa Ya Kaddamar Da Rumbun Sauki Don Sayar Wa Ma’aikata Kayayyakin Abinci A Farashi Mai Rahusa A Sakkwato
- DHQ Za Ta Tura Dakaru Na Musamman 800 Yankunan Da Ke Fama Da Rashin Tsaro – CDS
Gwamna Abba Yusuf ya taya al’ummar Musulmi a fadin jihar murnar ganin sabuwar shekarar Musulunci da ta fara da watan Muharram.
Ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da sauran al’ummar Kano da su yi amfani da wannan dama wajen yin tunani a kan ayyukan da suka yi a cikin shekarar da ta gabata, tare da yin addu’o’in zaman lafiya da hadin kai da ci gaba a jihar da kasa baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp