Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta bayyana matukar adawa da yadda NATO ta yi amfani da kasar Sin a matsayin dalilinta na neman fadada zuwa yankin Asia da Pasifik.
Kakakin ma’aikatar Zhang Xiaogang ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis, lokacin da yake tsokaci game da furucin sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO.
A cewar Zhang Xiaogang, kasar Sin na nace wa bin hanyar samun ci gaba cikin lumana, da manufar tsaron kasa. Yayin da ita kuma NATO ke mayar da hankali wajen tada hargitsi da takalar rikici da yake-yake a yankuna daban daban, ta yadda ta mayar da kanta mai ingiza yake-yake.
Ya ce Sin na bukatar NATO ta nazarci aikace aikacenta, ta sauya dabara, ta kuma bayar da karin gudunmuwa ga wanzuwar tsaro da kwanciyar hankali a duniya.
Game da furuci na baya bayan nan da sakataren tsaron Amurka ya yi, yana mai bayyana kasar Sin a matsayin barazana, da nanata shigar Amurka yankin tekun India da Pasifik domin wanzar da zaman lafiya ta hanyar amfani da karfi, kakakin ya bukaci Amurka ta fahimci kasar Sin ta hanya mai dacewa da sanin ya kamata, ta kauracewa karairayinta da yaudara dake karkatar da hankalin Amurkawa da na duniya. Ya ce kasar Sin bata taba amfani da ci gabanta wajen yi wa wata kasa barazana ba, kuma bata matsin lamba ko muzgunawa kamar yadda wata kasa ke yi, yana cewa rundunar sojin Sin karfi ne na tabbatar da zaman lafiya a duniya. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp