• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wata 6 Da Haramta Kauyawa Day A Kano: Badalar Na Ci Gaba Da Gudana 

by Abdullahi Muh'd Sheka
4 months ago
Kano

Babban abin damuwa ne da kuma jimami, kan yadda jihar Biniwe, ta zama fagen dagar zubar da jinin bil’ Adama, wanda hakan, ya sanya, jihar, ta shiga cikin zaman makoki, na rayukan da aka hallaka, musamman bayan munanan hare-haren da aka kitsa, tare da kaiwa kan alummomin da ke a  Yelewata da Daudu, da ke a karamar hukumar Guma, ta jihar.

Lamarin ya yi sanadiyyar rasa rayuka sama da 100, dubban wasu kuma, suka samu raunuka, tare da tarwatsa wasu jama’a, daga matsugnansu, ko kuma suka bace bat.

  • Kano Ta Ayyana Ranar Alhamis Hutu Domin Murnar Sabuwar Shekarar Musulunci
  • Ƴansanda Sun Gano  Ƙarin Bama-Bamai 9 Da Basu Fashe Ba A Kano

Karin wani abin takaicin shi ne, bayan sa’oi 48 da kai harin a wadannan yankunan, an kuma sake kai wani sabon harin a wasu yankunan, da ke a karamar hukumar Makurdi, inda aka halaka mutane 25

Wasu bayanai sun nuna cewa, wadannan kai hare-haren na dabbanci, an kitsa su, bisa nufin kisan kare dangi, musamman domin nuna kiyayya.

Wadannan hare-haren a jere, sun nuna cewa, tamkar, an yiwa jihar kawanya ne, wanda kuma hakan a zahiri, ya nuna gazawar, nauyin da ke kan mahukuntan jihar, na kare rayuka da kuma dokiyoyin ‘yan jihar.

LABARAI MASU NASABA

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

Misali, a lokutan hare-haren, an kone gidaje da dama, inda wasu ahali ma, wanda yawansu ya kai, har zuwa 15, aka shafe su, daga doron kasa, a lokacin da suke kan bacci, a gidansu.

Wasu daga cikin wadanda suka tsallake Rijiya da baya daga hare-haren na ‘yan ta’addar, sun bayyna yadda ‘yan ta’addar, suka cinnawa wasu shaguna da ke a wata kasuwa, da ka mayar a matsayin wajen kwanan, ‘yan gudun hijira, wuta.

Duk da kokarin da wasu matasa da kuma kokrin jami’an tsaro na dakile maharani, hakan ya faskare su, hatta wani daya daga cikin jami’in tsaro da aka tura wanzar da tsaro, ya rasa ransa.

Duk a 2025, a watan Afiiru an kai hare-hare a Logo da Ukum, inda aka kashe sama da 50.

Abin takaicin shi ne, duba da cewa akasarin masu kai hare-haren, sai sun sanar sanar suke kai hare-haren.

A gafe daya kuma, shuwagabbin alumma a wadannan yankunan su kan ankarar da hukumomi kafen kai hare-haren, amma abin takaici, mahukuntan, ba su daukar matakan dakile kai hare-haren.

A kwanan baya, Shugaba Bola Tinubu, ya umarci manyan Hafshoshin sojin kasar, da su gaggauta, kawo karshen kai hare-haren, tare da dawo da zaman lafiya a jihar.

Kazalika, ya danganta kashe-kashen, a matsayin na rashin imani da janyo koma baya, inda kuma ya yi kira ga jagororin ‘yan siyasa da shuwagabanin alumomi da ke a jihar, musamman a yankunan da lamarin yafi yin kamari, da su dakatar da rura wata, kan rikice-rikicen, musamman kan yadda suke furta kalaman kiyayya.

Fafaroma, Leo na 14, a na sa bangaren, ya yi tir da kashe-kashen a jihar, inda ya danta lamarin da kisan Kiyashi.

Hakazalika, Gwamnan jihar Hyacinth Alia, a martaninsa, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kawo wa jihar dauki, wanda ya yi nuni da cewa,  Biniwe ba wai dokar ta baci take bukata ba, daukin gaggawa take bukata, ta hanyar tura jami’an tsaro da kayan aiki, domin a yaki, masu kai hare-haren.

Sai dai, wannan furucin na gwamnan, tamkar holoko ne, kawai, domin alummar jihar, sun gaji, da yin wani zaman makoki, sun fi bukatar, a samar masu da jami’an tsaro, su kuma koma su ci gaba da noma gonakansu, suna kuma son su ci gaba da barcinsu, da idanuwansu, biyu, a rufe, ba tare da wata fargabar, za a kai masu hari a yayin da suke kan yin barcinsu ba.

A gafe daya kuma, ana ci gaba da cacar baki a tsakanin Gwamna Alia da wasu jiga-jigai na jihar, inda Gwamnan a kwanan baya, ya yi zargin cewa, akwai wasu ‘yan siyasar jihar, da ke zaune Abuja, suke ci gaba da kara rurar wutar rikici a jihar, ciki har da ma wasu jiga-jigan ‘yan Majalisar kasa da suke wakiltar mazabunsu, a majalisar.

Koda yake dai, ‘yan Majalisar, sun karyata wannan ikirarin na Gwamnan, inda suka zargi Alia, da kin wanzar da dokar barin yin kiwo a bainar jama’a a jihar.

Bai wai kawai cafko masu aikata ta’asar ya kamata ayi, ya zama wajibi, a hukunta su, kamar yadda dokar kasar, ta tanada.

Bugu da kari, dole ne Gwamnatin Tarayya, ta gagauta daukar matakai, tare da kuma taimakawa Gwamnatin jihar, domin ta samu karfin tarwatsa masu kai wa alumomin, hare-haren da kare alumomin.

Ya kuma zama wajbi, a sake yin nazari, kan batun iyakokin jihohi da batun burtanin masu kiwon dabbobi da kuma karfafa dangantaka, a tsakanin Fulani makiyaya da sauran alumomin da ke a jihar.

Hakazalika, ya zama wajibi, Gwamnatin Tarayya ta hada taron tattaunawa na kasa, kan batun na kai hare-haren.

Wannan Jaridar, ita ma, ta bi sahun sauran ‘yan Nijeriya, wajen mika ta’aziyyarta, bisa rasa rayukan da hare-haren ya rutsa da su tare da kuma kira da a dauki matakan gaggawa kan batun, ba wai kawai, yin bayanai ba.

Lokaci ya yi, da za a kawo karshen rikice-rikice da nuna kiyaya, a tsakanin juna.

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi
Labarai

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza
Labarai

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar
Labarai

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Next Post
Amince Wa Al’umma Mallakar Makamai Zai Ƙara Tsananta Rashin Tsaro — IGP

Amince Wa Al’umma Mallakar Makamai Zai Ƙara Tsananta Rashin Tsaro — IGP

LABARAI MASU NASABA

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

October 19, 2025
Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

October 19, 2025
Yadda Ake Alkaki

Yadda Ake Alkaki

October 19, 2025
Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (2)

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.