Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da duk wani shigo da kayan ƙarafuna daga jihohin Arewa maso Gabas zuwa jihar, bisa dalilin haɗarin da hakan ke janyowa. Wannan mataki ya biyo bayan fashewar wani abu da aka danganta da kayan ƙarafunan da aka kawo daga yankin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu da dama a Kano.
Kwamishinan Tsaro na jihar, Air Vice Marshal Ibrahim Umaru (mai ritaya), ne ya sanar da hakan a wata ganawa da manema labarai a ranar Laraba, inda ya ce bincike ya nuna cewa wasu abubuwan fashewa da aka ɓoye a cikin kayan bola ne daga Arewa maso Gabas ne suka haddasa wannan mummunar fashewar. Ya ce haramta shigo da irin waɗannan kayayyaki mataki ne na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
- Tinubu Ya Ƙaddamar Da Cibiyar Fasahar Da Aka Lalata Lokacin Zanga-Zanga A Kano
- Farfesa Haruna Musa Ya Lashe Zaɓen Shugabancin Jami’ar Bayero Ta Kano
“Mun umurci duk masu cinikayyar ƙarafunan bola da su dakatar da shigo da kaya daga Arewa maso Gabas nan take. Duk wanda aka samu da karya wannan doka zai fuskanci cikakken hukunci, ”in ji Umaru.
Ya jaddada cewa gwamnati ba ta hana kasuwancin kayan ƙarafunan bola gaba ɗaya ba, sai dai matsalar tana fitowa ne daga shigo da kayayyaki daga wuraren da ke fama da rikice-rikice ba tare da cikakken bincike ba.
Umaru ya bayyana cewa wannan matakin zai ci gaba da aiki har zuwa lokacin da za a bayar da sabuwar sanarwa, inda ya ce rashin kula wajen shigo da kaya daga yankunan da ke da haɗari na iya jefa rayuwar mutane da dama cikin hatsari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp