A yau Alhamis ne mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya halarci bikin bude dandalin tattaunawa kan zaman lafiya na duniya karo na 13, a jami’ar Tsinghua inda kuma ya gabatar da jawabi.
A cikin jawabin nasa, Han Zheng ya bayyana cewa, a halin yanzu an samu babban sauyi a duniya, tare da fuskantar batutuwan kasa da kasa da yankuna da dama, don haka ana fuskantar kalubale a sha’anin kiyaye zaman lafiya da samun ci gaban duniya.
Ya ce, tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama, da kiran samun bunkasar duniya, da kiran kiyaye tsaron duniya, da kuma kiran kiyaye al’adun duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, sun samar da ra’ayoyin Sin kan daidaita manyan batutuwan duniya dake shafar zaman lafiya, da bunkasa rayuwar bil’adama baki daya.
Han Zheng, ya gabatar da shawarwari hudu, inda da farko ya ce kamata ya yi a koyi fasahohi daga abubuwan da suka gabata, da tabbatar da odar kasa da kasa bayan yakin duniya na 2. Na biyu kuma a ci gaba da yin hadin gwiwa wajen sarrafa harkokin duniya baki daya. Na uku a kiyaye bude kofa ga kasashen waje, don sa kaimi ga samun wadata da ci gaba a duniya. Kana na hudu a goyi bayan juna don cimma nasarar zamanantarwa tare. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp