Tsohon ministan matasa da wasanni na Nijeriya, Solomon Dalung, ya yi ikirarin cewa an zaɓi nagartattun mutane domin jagorantar sabuwar jam’iyyar adawa ta ADC.
Dalung, wanda minista ne a lokacin tsohon shugaban ƙasa Muhammad Buhari, ya bayyana hakan ne a gidan talabijin na Channels a yammacin jiya Alhamis.
- ‘Yan Nijeriya Na Kewar Buhari Saboda Azabar Da Suke Fuskanta A Hannun Tinubu – Amaechi
- Bayan Taron Haɗaka, Hankali Wike Ya Tashi — ADC
A cewarsa, babu wani bidiyo da ya nuna sabon shugaban jam’iyyar ta ADC, Sanata David Mark yana cusa dala a cikin aljihunsa, ba kamar shugabannin wasu jam’iyyun ba.
Dalung ya ƙara da cewa haɗakar ƴan siyasar da suka koma jam’iyyar ADC ba ƙwace jam’iyyar suka yi ba kamar yadda wanda ya yi wa jam’iyyar takarar shugaban ƙasa a shekara ta 2023 Dumebi Kachikwu ya yi zargi.
Sai dai ya ce tsohon shugaban jam’iyyar Ralph Nwosu ne da kansa kuma a hukumance ya bayar da ragamar shugabancin jam’iyyar ga shugaba na riƙo, David Mark, da sakataren jam’iyyar na riƙo, Rauf Aragbesola.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp