Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce yaki ba zai warware batun nukiliyar Iran ba, kuma kaiwa kasar hare-hare, ba tare da ta aikata hakan ba ya sabawa doka.
Wang Yi, wanda ya bayyana hakan a jiya Juma’a, yayin taron manema labarai na hadin gwiwa tare da takwaransa na kasar Faransa Jean-Noel Barrot a birnin Paris, ya jaddada cewa, amfani da karfin soji ba abun da zai haifar sai ingiza karuwar tashin hankali da rura wutar kiyayya.
- Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu
- Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
Game da tambayar da aka yi masa dangane da yanayin da ake ciki a gabas ta tsakiya kuwa, Wang ya ce matsayin Sin game da batun nukiliyar Iran a bayyane yake, bai kuma sauya ba, cewa Sin na dora muhimmancin gaske kan alkawura a fili da jagororin kasar Iran suka sha dauka, na cewa kasarsu ba za ta kera makaman nukiliya ba.
Ya ce a lokaci daya kuma, Sin na martaba hakkin Iran na amfani da makamashin nukiliyarta bisa hanyoyi na zaman lafiya, kasancewarta wadda ta sanya hannu kan yarjejeniyar kasa da kasa ta hana yaduwa makaman nukiliya.
Karkashin hakan, ya dace sassan da batun ya shafa su gaggauta hawa teburin shawara, dangane da burin cimma sabuwar yarjejeniyar kasa da kasa ta warware batun Iran, da sanya daukacin harkokin nukiliyar kasar karkashin kulawa, da kariyar hukumar lura da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ko IAEA.
Taken cimma “Zaman lafiya ta amfani da karfi”, na dogaro ne ga siyasar nuna karfin tuwo, don haka Wang ya aza tambayar cewa, idan har karfi ne ke iya tabbatar da daidai da kuma kuskure, ta yaya za a iya tabbatar da dokoki da adalci? Kana ta yaya kasashe marasa karfi, musamman kanana da matsakaita za su iya rayuwa? (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp