Fadar Shugaban Ƙasa ta shawarci ‘yan adawar jam’iyyar ADC da su manta da burin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Sunday Dare, ya ce waɗanda ke shirin yin takarar ba su da komai face son zuciya, ba don amfanin ƙasa ba.
- Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa
- Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu
Ya bayyana a fili cewa: “Babu gurbi a Aso Rock har sai 2031.”
Dare ya soki haɗakar ‘yan adawa, inda ya bayyana cewa babu ɗaya daga cikinsu da ke da ƙarfi ko goyon bayan jama’a da zai iya lashe zaɓe.
Ya kwatanta ‘yan adawar da irin tsoffin guzumayen da suka rasa gurbi a siyasa.
Ya kuma yi watsi da koke-koken da suke yi na rashin adalci a tsarin mulki, inda ya bayyana hskan hakan da “labaran tatsuniya na siyasa” da ake amfani da su don yaudarar jama’a.
A cewarsa, gwamnatin Shugaba Tinubu tana da ƙarfi, tsari da kuma goyon bayan jama’a.
“Duk wanda ke shirin tunkarar 2027, zai fi dacewa ya tara a 2031,” in ji Dare.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp