Chelsea ta samu nasarar zuwa wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya na ƙungiyoyi bayan ta doke Fluminense da ci biyu da babu.
Sabon ɗan wasan Chelsea, Joao Pedro, wanda aka siya daga Brighton, ne ya ci ƙwallaye biyu a wasan.
- Malaman Firamare Sun Janye Yajin Aiki A Abuja, An Umarci Su Koma Bakin Aiki
- Babatun Lai Ching-Te Ba Zai Taba Girgiza Kasancewar Sin Day Tak A Duniya Ba
Wannan ne karon farko da ya fara wasa tun zuwansa Chelsea.
Ya jefa ƙwallo ta farko a minti na 18 bayan tsohon ɗan Chelsea, Thiago Silva, ya kasa fitar da wata ƙwallo.
Daga baya kuma ya ƙara ta biyu a minti na 56.
Wannan nasarar ta sa Chelsea ta ƙara samun kuɗi fam miliyan 22 wanda ya ƙaru kan fam miliyan 60 da suka riga suka samu a gasar.
Hakan yana nuna cewa suna samun riba daga siyan Joao Pedro da suka yi a fam miliyan 55.
Fluminense ta nuna rashin jin daɗi lokacin da alƙalin wasa ya soke bugun daga kai sai gola da aka ba su, bayan duba na’urar VAR.
Amma Chelsea na fuskantar damuwa da yiwuwar raunin ɗan wasan tsakiya Moises Caicedo ya samu.
Chelsea za ta kara da Real Madrid ko Paris Saint-Germain a wasan ƙarshe a ranar Lahadi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp