Tattalin arzikin kasar Sin ya nuna juriya mai karfi a cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14 a tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, inda aka yi hasashen karuwarsa za ta zarce yuan tiriliyan 35, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 4.89.
A wani taron manema labarai da aka gudanar yau Laraba, shugaban hukumar raya kasa da yin gyare-gyare, Zheng Shanjie, ya bayyana cewa, a cikin shekaru hudun farko na tsakanin lokacin, tattalin arzikin kasar ya habaka bisa matsakaicin karuwa da kaso 5.5 bisa dari a kowace shekara.
Zheng ya ce, duk da girgizar da annobar cuta ta haifar da kuma cin zarafi a bangaren kasuwanci, ci gaban da kasar Sin ta samu wata nasara ce da ba a taba ganin irinta ba idan aka yi la’akari da girman tattalin arzikinta.
Da yake karin haske game da babban ci gaban tattalin arzikin da aka samu, Zheng ya ce, jimillar kudaden da aka kashe a bangaren bincike da aiwatarwa na kasar ya haura kusan kashi 50 cikin dari, watau adadin yuan tiriliyan 1.2, daga shekarar 2020 zuwa 2024, kuma kamfanoni masu zaman kansu da suka yi rajista sun zarce miliyan 58 a karshen watan Mayun 2025, adadin da ya dara na 2020 da fiye da kashi 40 cikin dari. (Abdulrazaq Yahzua Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp