Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar ta samu nasarar yanke hukunci ga ƴan ƙasashen waje 146 daga cikin 194 da aka kama kan laifukan damfara ta yanar gizo da suka shafi tattalin arziƙin ƙasa. Ya bayyana hakan ne yayin buɗe taron ƙasa da ƙasa kan tsaro na yanar gizo da Hukumar NITDA ta shirya a Abuja ranar Laraba.
Olukoyede ya ce waɗanda aka yanke wa hukunci sun aikata laifuka ne ta hanyar amfani da shaidar ƙarya ta ƴan Nijeriya domin damfarar mutane da hukumomi. Ya ce hakan yana jefa ƴan Nijeriya cikin shakku da zargi a idon duniya duk da cewa ba su da hannu a cikin laifin.
- EFCC Ta Gurfanar Da Wasu Kamfanoni Biyu Gaban Kuliya Bisa Damfarar Naira Miliyan 80
- Ni Ne Na Kai Kaina ga Hukumar EFCC, In Ji Tsohon Jami’in NNPC
Ya tabbatar cewa bayan kammala zaman gidan yari, za a mayar da waɗannan ƴan ƙasashen waje zuwa ƙasashensu. Ya kuma yaba da irin goyon bayan da hukumomin FBI, da Interpol da sauran hukumomin tsaro na duniya suka bayar domin ganin an samu nasara a gurfanar da waɗannan masu laifi.
Shugaban EFCC ya sanar da shirin ƙaddamar da wata sabuwar cibiyar tsaron yanar gizo da za ta riƙa gano hare-haren yanar gizo cikin awa ɗaya, domin daƙile ayyukan masu kutse cikin lokaci ƙanƙani. Ya ce laifukan yanar gizo na ci gaba da rikiɗa kuma suna ƙara samun gindin zama a faɗin duniya.
A ƙarshe, Olukoyede ya bayyana cewa EFCC na shirin buɗe wata cibiyar bincike da gyaran hali da za ta tallafa wajen sake tarbiyyar waɗanda aka kama da laifukan yanar gizo. Ya buƙaci haɗin kai daga bankuna, da hukumomin tsaro da na kuɗi don yaƙar wannan matsala mai girma ga ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp