• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yakin Afghanistan Ba Fim Ba Ne

byCMG Hausa
3 years ago
Afghanistan

“Dana daya ya fado daga jirgin sama a filin jiragen sama na Kabul, dayan kuma har yanzu ba mu san inda yake ba”.

Kalaman da Mohammad Rezayee, dan kasar Afghanistan ya yi a kwanan baya a yayin da yake tattaunawa tare da jaridar The Times ta Burtaniya a kwanan baya, sun tunatar da mu kan abin da ya faru a shekara daya da ta gabata.

  • Nijeriya Da Amurka Sun Kulla Yarjejeniyar Dawo Da Kudaden Da Abacha Ya Wawure

A watan Agustan shekarar 2021, Amurka ta janye sojojinta daga kasar Afghanistan ba tare da daukar nauyin da ke bisa wuyanta ba, matakin da ya sa dubu dubantar ‘yan Afghanistan suka kutsa cikin filin jiragen sama na Kabul, inda jiragen saman dakon kaya na sojan Amurka suka tashi ba tare da yin la’akari da yadda ‘yan Afghanistan ke kokarin neman shiga jiragen, matakin da ya sa mutane da dama suka fado daga jirgin, kuma Zabi Rezayee mai shekaru 17 da haihuwa kuma dan Mohammad Rezayee, na daya daga cikin wadanda suka fado, a yayin da Zaki Rezayee, dansa na daban wanda a lokacin shi ma ya ke kan jirgin, amma an rasa inda yake.

Yanzu iyalan Mohammad Rezayee na fuskantar kuncin rayuwa, sun sayar da kadarorinsu, kuma ba yadda za su yi su rufe shagon sai da ‘ya’yan itatuwa da ganyayen lambu da suka gudanar, duk da haka, wani lokaci ba su iya biya kudin burodi ba.

Abin da ya faru ga Mohammad Rezayee, yana kuma faruwa ga sauran ‘yan kasar ta Afghanistan.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Duk da cewa, a karshen watan Agustan bara, Amurka ta dasa aya ga yakin Afghanistan da ya tayar bisa sunan “yaki da ta’addanci”, amma ga mawuyacin halin da yakin ya haifar ga al’ummar kasar.

Baya ga haka, duk da cewa Amurka din ta janye sojojinta, amma tana ci gaba da kakaba wa kasar takunkumi, har ma ta haramta al’ummar kasar da ke fama da kunci yin amfani da kudadensu tare da neman satar wani kasonsu, lamarin da ya haifar da matsalar jin kai mai tsanani a kasar.

David Howell Petraeus, tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasar Amurka, ya taba amincewa da laifin da Amurka ta aikata cikin shekaru 20 da suka wuce a yayin da ta tura sojojin zuwa Afghanistan, kuma a yayin da ya tabo magana a kan yakin Afghanistan, ya kan ce, “ya yiwu ka gaji da kallon wani fim, kuma ka bar gidan sinima, a yayin da kuma fim din na ci gaba”.

Sai dai yakin Afghanistan ba fim ba ne. Yakin da Amurka ta kaddamar a Afghanistan cikin shekaru 20 da suka wuce, ya lalata kasar da kuma makomar al’ummar kasar, tare da halaka mutane dubu 174, ciki har da fararen hula sama da dubu 30, baya ga kuma miliyoyin al’ummar kasar suka zama ‘yan gudun hijira.

Lallai Amurka ta tafi bayan da ta gaji da yakin, amma da wuya a kawar da raunin da ya haifar ga al’ummar Afghanistan, wadanda yanzu haka miliyan 18.0 ke matukar fama da matsalar karancin abinci, kuma yara miliyan 3 sun kasa samun damar shiga makaranta.

Nan da wasu kwanaki, za a cika shekara guda da Amurka ta janye sojojinta daga Afghanistan.

Ya kamata gwamnatin Amurka ta yi na’am da laifukan da ta aikata, kuma ta dauki matakan da suka wajaba don biyan hasarorin da al’ummar Afghanistan suka sha.

Wani abu da ya fi muhimmanci kuma shi ne, bai kamata a manta da yakin Afghanistan ba, musamman ma kasar Amurka, dole ta yi koyi darasi daga yakin. (Mai zane:Mustapha Bulama)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Next Post
Yajin Aiki Zai Ci Gaba Tun Da Gwamnati Ta Kasa Dauki Matakin Da Ya Dace – ASUU

Yajin Aiki Zai Ci Gaba Tun Da Gwamnati Ta Kasa Dauki Matakin Da Ya Dace – ASUU

LABARAI MASU NASABA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version