Albarkacin taron ministocin kasa da kasa na tattauna mu’ammalar wayewar kai ta duniya, CGTN ta hada hannu da jami’ar Renmin ta kasar Sin, domin jin ra’ayin al’ummun kasashe 41 da yawansu ya kai dubu 12.
Masu bayyana ra’ayoyin na ganin cewa, mu’ammala, da cudanyar al’adu, da wayewar kai muhimmin karfi ne na ciyar da bunkasar wayewar kan daukacin bil’adama da zaman lafiyar duniya gaba, don haka ne ma darajanta al’adu da magabata suke dora muhimmanci a kanmu, da kirkire-kirkire, na da babbar ma’ana ga zamanantar da al’ummun bil’adama, wanda hakan ya sa shawarar bunkasa al’adun duniya da Xi Jinping ya gabatar, ta samu karbuwa tsakanin sassan kasashe daban-daban, yayin da suke kokarin tinkarar kalubaloli a duniya.
Yayin da aka tabo batun fahimtar alamun al’adun Sinawa, kashi 60.6% daga cikin mutanen da aka jin ra’ayinsu, na mai da batun kirkire-kirkire a gaban komai. A ganinsu kirkire-kirkire a bangaren kimiya na jawo hankulansu matuka. Kazalika, kaso 77.2% daga cikinsu sun fi mayar da matukar hankali kan kimiyar Sin, da yadda ake amfani da ita, fiye da mayar da hankula kan zamantakewar Sinawa, da al’adun gargajiya, da al’adu na zamani na kasar Sin. Dadin dadawa, kaso 81.6% daga cikinsu na ganin cewa, tasirin al’adun Sin sun rika karuwa a duniya, kuma fiye da kashi 80% na matasan da aka ji ra’ayinsu ’yan kasa da shekaru 44, su ma sun amince da wannan ra’ayi. Kana kashi 70.6% na ganin cewa, wayewar kan Sinawa, ta bullo da wata sabuwar hanyar daidaita harkokin duniya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp