Shugaban kungiyar masu nakasa ta fuskar datsattsen lebe da handa na Nijeriya (NACLP), Farfesa Nnadozie Ugochukwu, ya bayyana rashin jin dadinsa, kan yadda ake amfani da yara masu nakasa a lebe wajen yin tsafi da su.
Ya bayyana kalubalen kiwon lafiya da ke da alaka da jariran da aka haifa a matsayin babban kalubale a Nijeriya, inda ya bayyana cewa; wasu lokutan ana ganin yaran da ke fama da wannan matsala a matsayin kamar ‘ya’yan da shedanu ke dauke da su, shi yasa mafi yawan lokuta ake sadaukar da su (Tsafi).
- An Kama Magungunan Jabu Na Fiye Da Naira Biliyan Ɗaya A Kano
- An Bude Taron Ministoci Kan Wayewar Kai A Birnin Beijing
Da yake zantawa da manema labarai a taron kimiyya karo na 6 da aka gudanar da kuma taron shekara na 2025 (AGM), wanda ya gudana a babban asibitin kashi na kasa da ke Jihar Inugu, shugaban kungiyar ya shawarci mata masu juna biyu da su rika kula da zuwa awon ciki yadda ya kamata.
Kazalika, ya bukaci gwamnati a dukkan matakai a Nijeriya da ta fara ba da kulawa sosai wajen tunkarar kalubalen lafiyar Dan’adam da ke da alaka da jariran da aka haifa.
“Har yanzu, wannan babban kalubale ne a Nijeriya, domin kuwa ana ganin wadanda aka haifa da nakasa a lebe a matsayin jariran da shedanu ko aljanu ke dauke da su, wani lokacin kuma ana sadaukar da su ko a yi tsafi da su; wanda ko shakka babu, wannan batu ya haifar da rushewar gidaje da dama da kuma mutuwar aure.
“A wajen jahilai, tsagaggen lebe lahani ne a kan makogwaro da lebe, amma idan akwai shinge tsakanin hanci da baki, ana kiran sa da suna handa. Wani abu ne da ba a san abin da yake kawo shi ba, amma kuma ana danganta shi da abubuwa da dama kamar karancin rashin sinadarin bitamin B.”
“Don haka, muna shawartar mata masu juna biyu da su mayar da hankali wajen yawan zuwa awon ciki, sannan kuma su rika shan magungunan da ake ba su na yau da kullum, ta yadda za a rage haihuwar masu dauke da wannan cuta.
“Hakika wannan babban abin takaici ne a cikin al’umma, shi yasa kwararrun likitoci, ma’aikatan jinya, jami’an jin dadin al’umma da likitocin makogwaro, hanci da kunne suka taru, domin ganin abin da za mu iya yi da zai kawo wa al’umma sauki tare da karfin tattalin arziki a tsakaninsu a wannan kasa”, in ji shi.
Har ila yau, da yake zantawa da manema labarai, Daraktan kula da lafiya na asibitin kashi na kasa da ke Jihar Inugu, Farfesa Emmanuel Iyidiobi ya bayyana cewa; kulawa da masu matsalar tsagaggen lebe, na daya daga cikin manyan manufofin da wannan asibiti ya sanya a gaba don ganin ya cimma, yana mai jaddada cewa; wani bangare ne na aikin tiyata, ya gara da cewa, wasu daga cikin sassan sun hada da kula da wadanda suka kone, tiyata da dai sauran makamantansu.
“Mun yi hadin gwiwa da kungiyar ‘Smile Train’ fiye da shekara goma da ta wuce, domin kula da marasa lafiya. Kazalika, zan iya fada muku cewa; bayanai sun nuna cewa, mun fi kowane asibiti a Nijeriya yawan yin wa marasa lafiya tiyata”.
“Don haka, ba wani abu ba ne na daban don mun karbi bakuncin wannan taro na bana, sannan kuma mun ji dadin yin hakan kwarai da gaske. Kazalika, me yasa muke yin hakan? Da farko dai, hakan ya yi daidai da muradun shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
“Sannan, sabon kudirin nan na shugaban kasar game da kiwon lafiya, ya mayar da hankali tare da karfafa asibitoci wajen inganta harkokinsu ta hanyar horaswa da bincike ta yadda daga wasu kasashen na waje za a rika zuwa a matsayin yawon bude ido tare da neman lafiya a wannan kasa, shi yasa muka yanke shawarar tallafa wa taron ka’in da na’in”, in ji shi.
Har ila yau, a nata jawabin, mataimakiyar shugabar kungiyar ‘Smile Train’, Darakta a shiyyar Afirka, Madam Nkeiruka Obi ta ce; kungiyar ta yi imanin cewa; duk yaron da aka haifa da matsalar datsattsen lebe, ya cancanci samun cikakkiyar kulawa daga kwararru, wadanda suka samu horo a cikin gida Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp