Shugaban Nauru David Ranibok Adeang ya bayyana yadda kasar Sin ta samu ci gaba, a matsayin darasi, abun koyo ga Nauru da sauran sassan duniya.
David Adeang, ya bayyana haka ne kwanan nan, yayin zantawarsa da ‘yar jaridar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG), yayin ziyararsa a kasar.
- Muhimmanci, Tasiri Da Kuma Amfanin Jigida Ga Mata
- Lauyoyin Natasha Sun Buƙaci Ta Koma Majalisa Ranar Talata Bayan Miƙa Takardun Hukuncin Kotu
A cewar David Adeang, a matsayinsa na shugaban kasa, aikinsa shi ne kokarin koyon darussa daga kasar Sin, musamman koyon muhimman dabi’un jama’ar kasar. Ya ce, wadannan dabi’u ne suka sa kaimi ga jama’ar kasar Sin wajen ba da gudummawarsu ba tare da son kai ba, da inganta ci gaban al’umma baki daya, da fitar da daruruwan miliyoyin mutane daga kangin talauci, da gina kasar Sin zuwa daya daga cikin kasashen da suka samu ci gaba a duniya a yau.
Yayin da yake magana kan alakar Nauru da kasar Sin, Adeang ya ce, karbuwar da ya samu a lokacin da ya zo kasar Sin ta sha bamban da irin wadda ya samu a lokacin da ya ziyarci sauran manyan kasashe. Yana cewa kasar Sin ta karbe shi kamar yadda za ta karbi wata kasa mai girma a duniya, inda ya ce Sin na nuna daidaito yayin mu’amala da kasa da kasa.
Ya kara da cewa, daga dawowar huldar diflomasiyya tsakanin Nauru da Sin, Nauru ta samu gagarumin sakamako na ci gaba da bunkasar tattalin arziki. Shugaban ya ce, yana da cikakken kwarin gwiwa game da raya dangantakar tattalin arziki da kasuwanci da kasar Sin.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp