Mataimakin firaministan Sin Ding Xuexiang, ya yi kira a karfafa hadin gwiwa a bangaren tattalin arziki na zamanni ko kuma tattalin arziki na dijital.
Ding Xuexiang ya bayyana haka ne jiya Juma’a, yayin da ya halarci bikin bude taron kungiyar kasashen hadin kai ta Shanghai (SCO) kan tattalin arzikin dijital, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin.
Cikin jawabinsa na bude taron, Ding Xuexiang wanda kuma mamba ne na kwamitin dindindin na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, bisa la’akari da damarmaki da kalubale da na’urori da fasahohin zamani suka zo da su, ya kamata a yi kokarin gaggauta aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen SCO suka cimma da kuma yarjejeniyar tafiyar da harkokin fasahohin zamani ta duniya.
Mataimakin firaministan ya kuma bayar da shawarar inganta hadin gwiwa a bangaren tattalin arziki na dijital da karfafa manufofin tuntubar juna da tsara burinkan ci gaba na kasashen ta yadda za su dace da juna da yin cikakken amfani da dandamalin hadin gwiwa kamar na taron na SCO kan tattalin arzikin dijital, domin kara wa kokarin raya bangaren kuzari. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp