Kakakin ma’aiktar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya yi watsi da zargin da kasar Japan ta yi, cewa wai wani jirgin saman soji na Sin ya yi shawagi kusa da nata jiragen, yana mai cewa bangaren Sin ya gudanar da ayyuka bisa doka da kwarewa.
Jiang Bin, ya bayyana hakan ne a Lahadin nan, yayin da yake amsa tambayar manema labarai kan batun, inda ya ce wani jirgin sama na tattara bayanan tsaron samaniya na Japan, ya yi shawagi kurkusa da yankin tsaron sama na Sin, daura da tekun gabashin kasar, kuma hakan ya sa jirgin saman soji na Sin ya dauki matakan tantancewa, da bin diddigi, da lura da ayyukan jirgin saman Japan bisa kiyaye doka.
Jami’in ya jaddada cewa, matakan da dakarun Sin suka dauka halastattu ne, an kuma gudanar da su bisa hangen nesa da nuna kwarewa da bin cikakkun ka’idoji. Kazalika, a cewarsa, sau da dama jiragen sama da na ruwa na Japan na kusantar yin kutse a yankunan Sin, wanda hakan ke haifar da barazana ga tsaron teku da sararin samaniyar sassan biyu.
Don haka Jiang Bin ya yi kira ga tsagin Japan, da ya yi aiki tare da bangaren Sin, wajen kyautata yanayin da zai samar da ci gaban dangantakar kasashen biyu bisa daidaito. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp