Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga madam Jennifer Simons, sakamakon nasarar da ta yi ta zama shugabar Jamhuriyar Suriname.
A sakon da ya aike ranar Jumma’a, shugaba Xi ya ce, Suriname abokiyar hadin-gwiwa ce ta kasar Sin bisa manyan tsare-tsare a yankin Caribbean. Kazalika, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakaninsu shekaru 49 da suka wuce, ya zuwa yanzu, sakamkon kokarin da kasashen biyu suka yi tare, dangantakarsu ta bunkasa lami lafiya, inda suka cimma nasarori da dama a fannoni masu yawa na hadin-gwiwa, tare kuma da kara tuntubar juna a harkokin kasa da kasa.
Xi ya kara da cewa, yana maida hankali sosai ga raya ci gaban huldar kasashen biyu, tare da bayyana fatan kara kokari tare da shugaba Simons, da zurfafa hadin-gwiwar kawo moriyar juna, da sa kaimi ga bunkasa dangantakar abokantakarsu ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare, don samar da alfanu ga al’ummun kasashen biyu. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp