Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana rayuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a ranar Lahadi 13, ga Yulin 2025 a matsayin babban rashi ga Nijeriya.
A wata sanarwa da ya fitar daga Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Obasanjo ya bayyana Buhari a matsayin aboki, abokin aiki, kuma ɗan ƙasa nagari wanda ya taka rawar gani a matsayin soja.
- Rasuwar Buhari: An Yi Rashin Ɗan Ƙasa Na Gari, Abin Koyi — Kungiyar Gwamnonin Arewa
- Tinubu Ya Tabbatar da Rasuwar Buhari, Ya Tura Shettima Zuwa Landan
Sanarwar, wadda mai taimaka masa wajen hulɗa da manema labarai, Kehinde Akinyemi, ya fitar, ta bayyana cewa Obasanjo ya samu labarin rasuwar tsohon shugaban ƙasa cike da alhini da juyayi.
Ya ce mutuwar Buhari ta zo a wani lokaci da ƙasa ke buƙatar kwarewar tsofaffin shugabanninta domin fuskantar ƙalubalen da take ciki.
“Cikin kaɗuwa da raunin zuciya na samu labarin rasuwar aboki na, abokin aiki, ɗan ƙasa nagari, Janar Muhammadu Buhari. A matsayinsa na soja ya taka muhimmiyar rawar a matsayin mai mulki, ya yi nasa aikin a matsayin dattijo, ya kuma bayar da gudunmawarsa.
“Wannan babban rashi ne ga ƙasa, domin a irin wannan lokaci muna buƙatar kwarewa da basira daga waɗanda suka taɓa jagorantar Nijeriya, don su taimaka mana mu fita daga halin da muke ciki.
“Abin da zan iya cewa shi ne: Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya karɓe shi cikin rahamarSa. Zamu yi matuƙar kewarsa. Allah Ya sa ya huta cikin salama,” cewar Obasanjo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp