A daren ranar Lahadi ne kungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta doke abokiyar karawarta ta PSG da ci 3-0 a wasan ƙarshe na gasar kofin Duniya na ƙungiyoyi da aka buga a filin wasa na Metlife da ke birnin New York, wasan ya samu halartar shugaba Donald Trump na ƙasar Amurka.
Ƙwallayen da Chelsea ta ci sun fito ta hannun Cole Palmer, wanda ya ci ƙwallaye biyu, sai kuma sabon ɗan wasan Chelsea Joao Pedro da ya ci ta uku kuma ta ƙarshe a wasan, Chelsea ta samu kyautar zunzurutun kuɗi har fam miliyan 125 daga hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) a sakamakon lashe kofin.
- Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani Game da Wasan Ƙarshe Tsakanin Chelsea Da PSG
- Kofin Duniya: Chelsea Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Ta Doke Fluminense
PSG ta kasa cin kofinta na 5 a wannan kakar wasannin ta bana, bayan ta lashe manyan kofuna 4 da suka haɗa da French Ligue 1 da French Super Cup da Cupe De France da kuma gasar zakarun Turai ta Uefa Champions League.
Wannan kofin da Chelsea ta ɗauka ya sa ta zama ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta farko a tarihi da ta lashe duka manyan kofuna da ake da su a harkar ƙwallon ƙafa tun daga, Premier League da FA Cup da EFL Cup da Champions League da Europa League da Conference League da kuma Club World Cup.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp