Aƙalla mutum huɗu ne aka tabbatar da rasuwarsu a yayin da wasu mutane bakwai suka jikkata a sakamakon rushewar wani ginin bene mai hawa uku a unguwar Abedi, Sabon Gari da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano.

Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano da ta NEMA, Saminu Yusif da Umar Madigawa, ne suka tabbatarwa da Jaridar LEADERSHIP HAUSA faruwar lamarin.
- Gwamnatin Kano Ta Gabatar Da Buƙatu 10 A Gaban Kwamitin Gyaran Tsarin Mulkin Nijeriya
- Kawu Sumaila Ya Yabi Gwamnatin Kano Kan Goyon Bayan Kirkiro Sabuwar Jihar Tiga
Sun bayyana cewa ginin ya rushe ne da yammacin ranar Lahadi bayan saukar ruwan sama mai ƙarfi.
Wasu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da ma’aikata masu gini da kuma masu wucewa da suka nemi mafaka a ƙarƙashin ginin da ba a kammala ba a yayin da ruwan saman ke sauka.
Madigawa ya ce ofishinsu na Kano ya karɓi kiran gaggawa da misalin ƙarfe 6:49 na yamma, kuma nan take suka ɗauki matakin kai ɗauki tare da haɗin guiwar hukumomi masu ruwa da tsaki.
Ya ƙara da cewa zuwa ƙarfe 11:30 na safiyar Litinin, an ceto mutane 11, ciki har da huɗu da suka rigamu gidan gaskiya, yayin da bakwai suka tsira da rai, kuma an garzaya da su Asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad da ke Kano don kulawar jami’an lafiya.
Yanzu haka, ana ci gaba da aikin ceto domin tabbatar da babu sauran waɗanda ke cikin ginin da ya ruguzo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp