Za a gudanar da bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin harin Japan da Sinawa suka yi da yakin kin tafarkin murdiya da al’ummun duniya suka samu a nan birnin Beijing. Kuma Sin na maraba da zuwan ’yan jaridar kasa da kasa don su labarta wannan muhimmin lokaci.
Dadin dadawa, Sin ta bude shafin yanar gizo mai adireshin http://kzjn80reg.zgjx.cn don saukaka yin rajista ga ’yan jaridar duniya da na yankunan Hongkong da Macao na Sin, kuma tana gayyatar ’yan jaridar da su yi rajista ta wannan hanya bisa gaggarumar maraba. Za a iya yin rajista ne daga raneku 15 zuwa 29 ga watan nan da muke ciki.
Ban da wannan kuma, Sin za ta kafa cibiyar yada labarai yayin bikin ta yadda ’yan jarida na gida da na waje za su tafiyar da aikinsu cikin sawaba. Cibiyar za ta sauke nauyin dake wuyanta na maraba da ’yan jarida da gabatar da tarukan manema labarai daban-daban da ba da jagoranci ga aikin neman labarai da kuma kafa shafin yanar gizo na cibiyar da na WeChat, ta yadda za a yi amfani da fasahar intanet don baiwa ’yan jaridar hidimomi. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp