Tsohon shugaban ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), ya bayyana marigayi Muhammadu Buhari a matsayin mutum mai cikakken riƙon amana da gaskiya, wanda za a iya yarda da shi a kowane lokaci kan kowane irin al’amari a duniya.
A wata hira da ya yi da manema labarai a birnin Landan, Abdulsalami ya bayyana cewa shi da Buhari sun kwana a asibiti ɗaya kafin rasuwar tsohon shugaban ƙasar, inda ya ce an sallame shi daga asibitin ne kwana kaɗan kafin ya samu labarin mutuwar Buhari a ranar Lahadi.
- Kasar Sin Ta Nuna Alhinin Rasuwar Tsohon Shugaban Nijeriya Buhari
- Gwamnati Ta Kafa Kwamitin Tsara Yadda Za A Binne Buhari
Ya ƙara da cewa dangantakarsu da Buhari ta samo asali ne tun daga rundunar Sojoji, inda suka shafe shekaru suna aiki tare. Ya bayyana Buhari a matsayin jagora mai nagarta, gaskiya da tsoron Allah, wanda ya kafa tarihi a rayuwarsa ta mulki da zaman rayuwa.
Janar Abdulsalami ya bayyana mutuwar Buhari a matsayin babban giɓi da zai yi wuya a cike, ba kawai ga Nijeriya ba har ma da dukan yankin Yammacin Afirka, inda ya ce Buhari ya kasance ginshiƙi na kwantar da hankali da ladabtar da gwamnati.
Ya kuma yaba da yadda Shugaba Bola Tinubu ya ɗauki lamarin da muhimmanci, yana mai cewa irin gaggawar da ya nuna wajen kafa kwamitin jana’iza da kiran zaman makoki ya nuna girman mutuncin Buhari a idon duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp