Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar zartarwa ta rundunar sojojin kasar Sin, ya gabatar da jerin abubuwa da ake bukata, da manyan kudurori da burika mafiya muhimmanci a ayyukan raya birane, yayin taron koli game da aiki a yau Talata a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Taron da aka bude a Talatar nan ya bayar da damar gabatar da humimman ayyuka bakwai na raya biranen kasar Sin. Na farko shi ne mayar da hankali ga cimma nasarar tsare-tsaren raya birane. Sai na biyu, wato gina managarcin tsari da kirkire-kirkire a fannin birane. Na uku kuma mayar da hankali ga gina birane masu dadin zama da walwala ga jama’a. Na hudu kuma, gina birane masu kyawun gani marasa gurbata yanayi, da fitar da karancin iskar carbon mai dumama yanayi. Kana na biyar mayar da hankali ga gina birane masu tsaro da za a iya dogaro da ingancinsu. Na shida kuma, karkata hankali ga gina birane masu tsarin wayewar kai, masu yanayi mai nagarta da karko. Yayin da na bakwai ya kasance mayar da hankali ga gina birane masu amfani da fasahohin zamani da gamsarwa. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp