• English
  • Business News
Thursday, July 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Wanke Fayose Daga Zargin Zambar Naira Biliyan 3.3

by Sadiq
19 hours ago
in Manyan Labarai
0
Kotu Ta Wanke Fayose Daga Zargin Zambar Naira Biliyan 3.3
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta wanke tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, daga tuhumar zambar kuɗi Naira biliyan 3.3. 

Mai shari’a Chukwujekwu Aneke, ya yanke hukuncin cewa hukumar EFCC ba ta gabatar da isassun hujjoji da za su tabbatar da laifin Fayose ba.

  • Yara 2 Sun KuÉ“uta Bayan Shafe Shekaru 6 A Hannun Boko Haram A Borno
  • EU, Turkiyya Da Sauran Ƙasashe Sun Yi Ta’aziyyar Rasuwar Buhari

Alƙalin, ya ce shaidun da EFCC ta kawo da takardun da aka gabatar ba su nuna Fayose ya aikata laifin ba.

Don haka, kotun ta amince da buƙatar Fayose na cewa babu hujja a kansa, kuma ta wanke shi daga duka tuhume-tuhume 11.

EFCC, ta zargi Fayose da karɓar Naira biliyan 1.8 daga hannun tsohon Ministan Tsaron Cikin Gida, Sanata Musiliu Obanikoro, ba ta hanyar amfani da banki ba.

Labarai Masu Nasaba

Atiku Abubakar Ya Fice Daga PDP, Duba Dalili

Peter Obi Ya Kai Wa Iyalan Buhari Ziyarar Ta’aziyya

Haka kuma, ta ce ya sayi kadarori a Legas da Abuja da kuɗaɗen da ake zargi na haram ne, sannan ya adana wasu maƙudan kuɗaɗe a asusun bankin kamfanoni da danginsa.

Fayose, ya musanta dukkanin waɗanda tuhume-tuhumen, inda ya ce kuɗin da ya karɓa na halal ne kuma ya yi amfani da su bisa doka.

Lauyoyinsa sun ce shari’ar tana da nasaba da siyasa kuma babu wata ƙwaƙƙwarar hujja a kanta.

Magoya bayan Fayose sun bayyana jin daÉ—insu kan hukuncin, inda suka bayyana cewa an samu nasarar yin adalci.

EFCC dai ba ta bayyana ko za ta ɗaukaka ƙara ba tukuna.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: EFCCEkitiFayoseKotuLegasZargi
ShareTweetSendShare
Previous Post

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

Next Post

Omokri Da Sarki Sun Soki Obi Saboda Rashin Halartar Jana’izar Buhari

Related

Atiku Abubakar Ya Fice Daga PDP, Duba Dalili
Manyan Labarai

Atiku Abubakar Ya Fice Daga PDP, Duba Dalili

14 hours ago
Peter Obi Ya Kai Wa Iyalan Buhari Ziyarar Ta’aziyya
Manyan Labarai

Peter Obi Ya Kai Wa Iyalan Buhari Ziyarar Ta’aziyya

15 hours ago
Nijeriya Na Fuskantar Siyasa Mara Tabbas —  Peter Obi
Manyan Labarai

Omokri Da Sarki Sun Soki Obi Saboda Rashin Halartar Jana’izar Buhari

17 hours ago
Kasa Da Wata Biyu Ya Bar Mulki, Shin Ko Buhari Ya Cika Wa ‘Yan Nijeriya Alkawarin Da Ya Yi Mu Su?
Manyan Labarai

EU, Turkiyya Da Sauran Ƙasashe Sun Yi Ta’aziyyar Rasuwar Buhari

23 hours ago
Mai Gaskiya Ya Koma Gida: Za A Yi Jana’izar Buhari A Daura
Manyan Labarai

Mai Gaskiya Ya Koma Gida: Za A Yi Jana’izar Buhari A Daura

2 days ago
Da ÆŠumi-ÆŠumi: Shettima Ya Isa Katsina Da Gawar Buhari
Da É—umi-É—uminsa

Da ÆŠumi-ÆŠumi: Shettima Ya Isa Katsina Da Gawar Buhari

2 days ago
Next Post
Nijeriya Na Fuskantar Siyasa Mara Tabbas —  Peter Obi

Omokri Da Sarki Sun Soki Obi Saboda Rashin Halartar Jana’izar Buhari

LABARAI MASU NASABA

Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Kafa Makomar Halittun Duniya Ta Bai Daya

Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Kafa Makomar Halittun Duniya Ta Bai Daya

July 16, 2025
Sojoji Sun Kashe Kwamandan Ƙungiyar Haram/ISWAP Da Wasu 5 A Chadi

Sojoji Sun Kashe Kwamandan Ƙungiyar Haram/ISWAP Da Wasu 5 A Chadi

July 16, 2025
Zambia Na Maraba Da Tawaga Ta 26 Ta Jami’an Lafiya Ta Sin

Zambia Na Maraba Da Tawaga Ta 26 Ta Jami’an Lafiya Ta Sin

July 16, 2025
Dubun Wasu Mutane 20 Da Ake Zargi Da Safarar Makamai A Kwara Ta Cika

Dubun Wasu Mutane 20 Da Ake Zargi Da Safarar Makamai A Kwara Ta Cika

July 16, 2025
Jarin Kasar Sin Ya Bada Gudunmawa Ga Ci Gaban Tattalin Arzikin Zimbabwe

Jarin Kasar Sin Ya Bada Gudunmawa Ga Ci Gaban Tattalin Arzikin Zimbabwe

July 16, 2025
Kwalejin Digiri Na Biyu Ta ABU Ta Ƙaddamar Da Sabbin Ɗalibai A Zariya

Kwalejin Digiri Na Biyu Ta ABU Ta Ƙaddamar Da Sabbin Ɗalibai A Zariya

July 16, 2025
An Gudanar Da Taron Ministocin Wajen Kasashe Mambobin SCO A Tianjin

An Gudanar Da Taron Ministocin Wajen Kasashe Mambobin SCO A Tianjin

July 16, 2025
PDP Ba Za Ta Damu Da Rashin Atiku Ba – Gwamna Makinde

PDP Ba Za Ta Damu Da Rashin Atiku Ba – Gwamna Makinde

July 16, 2025
Fasahar Amfani Da ’Yan Sandan Mutum-Mutumi Ta Kasar Sin Na Iya Taimaka Wa Tsaro A Afirka

Fasahar Amfani Da ’Yan Sandan Mutum-Mutumi Ta Kasar Sin Na Iya Taimaka Wa Tsaro A Afirka

July 16, 2025
Farashin Kayayyaki Sun Sauka A Watan Yuni 2025

Farashin Kayayyaki Sun Sauka A Watan Yuni 2025

July 16, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.