Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Fu Cong ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana fama da karin matsalolin sauye-sauyen yanayi a fadin duniya, tare da fuskantar kalubale a fannin aiwatar da jadawalin neman dauwamammen ci gaba zuwa shekarar 2030 na MDD. Don haka, ya kamata gamayyar kasa da kasa su tsaya tsayin daka, da karfafa hadin gwiwa, domin neman jituwa a tsakanin bil Adama da muhalin halittu, yayin kafa makomar halittun duniya ta bai daya.
Fu ya bayyana haka ne ranar Litinin, a yayin wani taro dake karkashin dandalin tattaunawar neman dauwamammen ci gaba na MDD da aka gudana a hedkwatar MDD dake birnin New York. Taken wannan taro shi ne, yadda kasar Sin ke aiwatar da manufar neman dauwamammen ci gaba zuwa shekarar 2030 da sakamakon da ta samu, wato yadda ra’ayin “Ruwa mai tsabta da koren tsauni, su ne tsaunin zinariya da na azurfa” ke inganta dauwamammen ci gaba a kasar Sin.
A cewarsa Fu Cong, daga shekaru 20 bayan gabatar da ra’ayin “Ruwa mai tsabta da koren tsauni, su ne tsaunin zinariya da na azurfa” zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta kasance kan gaba a duk duniya a fannonin rage makamashi mai gurbata muhalli da kyautata yanayin kasa, ta kuma kafa cikakken tsarin samar da sabbin makamashi mafi girma na duniya, yayin da ta ba da gudummawar dasa kaso 1 bisa 4 na sabbin itatuwa a duniya.
Haka zalika, kasar Sin ta samar da kaso 80 bisa dari na kayayyakin na’urorin samar da wutar lantarki daga zafin hasken rana ga duniya, da kaso 70 bisa dari, na kayayyakin na’urorin samar da wutar lantarki daga karfin iska, lamarin da ya ba da damammaki ga kasashe maso tasowa wajen raya kasa da amfani da sabbin makamashi kamar yadda suke bukata. A nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa da mu’amalar dake tsakaninta da bangarorin da abin ya shafa kan harkokin kare muhallin halittu, bisa shawarar bunkasa kasa da kasa, da shawarar “Ziri daya da hanya daya”, da inganta jadawalin neman dauwamemmen ci gaba zuwa shekarar 2030 na MDD. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp