Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Mauritania Mohamed Ould Cheikh Ghazouani, sun taya juna murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.
Xi ya ce, cikin shekaru 60 da suka gabata, ba tare da la’akari da sauye-sauyen yanayin kasa da kasa ba, a koyaushe bangarorin biyu suna mutunta juna da daukar junansu a matsayin daidai, tare da kafa wani abin koyi ta fuskar goyon bayan juna, da samun nasarar hadin gwiwa ga kowane bangare a tsakanin kasashe masu tasowa.
Xi ya kuma ce, yana mai da hankali sosai kan raya dangantakar da ke tsakanin Sin da Mauritania, kana yana son yin aiki tare da Ghazouani, wajen daukar cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya a matsayin wani sabon mafari don ciyar da dadaddiyar abokantakarsu gaba, da zurfafa amincewar juna da hadin gwiwa, da kuma bude wata sabuwar makoma ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Mauritania, ta yadda za a samar da karin moriya ga jama’ar kasashen biyu.
A nasa bangaren, Ghazouani ya ce, a cikin shekaru 60 da suka gabata, kasarsa da kasar Sin sun kulla zumunci mai kyau da ke nuna hadin gwiwa a dukkan matakai, da kuma nuna goyon baya ga juna a harkokin duniya.
Ya kara da cewa, a yayin taron kolin dandalin tattauna hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC na birnin Beijing da ya gudana watan Satumban bara, shi da shugaba Xi sun daukaka dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu zuwa matakin manyan tsare-tsare, inda ya bayyana matakin a matsayin wani lamari na zurfafa huldar da ke tsakanin kasashen biyu, wanda zai amfanar da jama’ar kasashen biyu ma’abota juna, da kuma taimakawa wajen inganta tsaro, da samun wadata da kyautata jin dadin al’ummomin sassan duniya.
Duk dai a wannan rana, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi musayar sakon taya murna da takwaransa na kasar Mauritania, Mokhtar Ould Diay. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp