Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya mayar wa da tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma babban jigo a jamiyyar PDP Alhaji Sule Lamido martani bisa kakkuasar sukur da Lamido ya yiwa Wike.
Wike wanda ya mayar da martanin ta hanyar mai taimaka masa na mussaman a kan harkar yada labarai Kevin Ebiri ya ce, Lamido a yanzu bai da wata kima a harkar siyasar kasar nan, inda ya kara da cewa, wadanda ke son su ha samun nasarar PDP a 2023, ba sa wani yin kokarin da ake bukata.
A cewarsa, Lamido na kawai son raba kan ‘ya’yan PDP ne, amma Wike ya bayar da gagarumar gudunmwa ga don ci gaba da dorewar PDP.
Ebiri ya ci gaba da cewa, Wike bai taba yin Ikirarin cewa akwai sama da kuri’u miliyan uku a jihar Ribas ba, amma Wike a matsayinsa na Jagoran PDP a jihar Ribas kuma Gwamnan da alummarsa ke son Sa, duk wanda ya ce zai yi jayayyar siyasa da Wike to fa shine zai sha kunya.
Ya kara da cewa, “Muna son mu tunatar da Lamido cewa, Wike bai sa kowa a cikin kwankwanto ba, a matsayin irin ikon da yake da shi wajen karkatar da kuri’un ‘yan jihar ga bangaren da yake gani zai amfani rayuwar alummar jihar Ribas, inda ya ce, idan Wike ya yi magana, alummar jihar Ribas na daukar maganar sa.
Ebiri ya kara da cewa, Alhaji Lamido ya dauka ‘yan Nijeriya sun manta da rawar da ya taka shi da ‘yan kanzaginta sa a tsakanin 2014 zuwa 2015, inda hakan ya janyo faduwar PDP a zaben 2015.
Ya ce, Wike a zaben 2015 ya kasance daga jamiyyar adawa ta PDP amma ya kayar da gwamna mai ci na APC Dakuku Peterside da kuri’u 1,029,102 , inda Dakuku yasha da kyat, da kuri’u 124,896.
Ebiri ya ce, “Muna shawartar ganin cewa, zaben 2023 ya matzo ya yi kokari ya dawo da jimarsa ta siyasa da ta zube ta hanyar kawo wa PDP kafatanin kuri’un ‘yan jihar Jigawa”.